1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta yanke wa wakiliyar DW hukuncin dauri

Kamaluddeen SaniNovember 26, 2015

Wata kotu a kasar China ta yankewa Gao Yu da ke wakiltar kafar yada labaru na DW a kasar hukunci daurin shekaru biyar tare da zaman daurin talala.

https://p.dw.com/p/1HD3A
Gao Yu
Hoto: picture-alliance/dpa/F. Singer

Kotun wacce tun da fari ta rage hukuncin zaman gidan yarin, ta kara da cewar 'yar jaridar mai shekaru 71 a duniya na da damar samun kulawar ja'mian lafiya.

A ranar alhamis din nan ce dai kamfanin dillancin labaran China ya bayyana cewar kotun ta amince da barin 'yar jaridar Gao damar kare wa'adin hukuncin da aka yanke mata daga wajen zaman gidan yarin a bisa dalilan al'amuran rashin lafiyar da take fuskanta.

Kazalika a cewar lauyan ta Mo Shaoping dake kareta a kotun dake a birnin Beijing yace iyalanta na iya daukar ta daga ofishin 'yansandan birnin don samun kulawar jami'an lafiya

Gao Yu dai an tsare ta ne tun a shekarar data gabata a bisa zargin sakin bayanan sirri ga kafofin yada labarai wanda lauyoyin ta suka musanta dukkanin zarge-zargen da hukumomin kasar suke mata.