1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ba ta ce uffan a kan yakin da Rasha ta kaddamar

Binta Aliyu Zurmi
February 25, 2022

A yayin da manya da kananan kasashen duniya ke daukar tsauraran matakai a kan Rasha, har ya zuwa wannan lokaci mahukuntan Beijing ba su kai ga cewa uffan ba a kan kaddamar da yaki da Rasha ta yi a kan Ukraine. 

https://p.dw.com/p/47Zie
China | Wladimir Putin und Xi Jinping
Hoto: Alexei Druzhinin/Sputnik/Kremlin Pool Photo via AP/picture alliance

A ganawar da ya yi da manema labarai a birnin Tokyo, jakadan Ukraine a Japan Sergiy Korsunsky na mai kira ga mahukuntan na China da su yi amfani da kyakyawar dangatakar da ke tsakanin su da Shugaba Vladimir Putin wajen kiran ya kawo karshen wannan rikicin da ba a san inda zai tsaya ba. Ya kara da cewar a wannan karni da muke ciki yaki ba shi ne maslaha ba.

Yayin da ake kira ga China na kokarin yin sulhu, a hannu daya a wannan Jumma'a za ta fara kwashe al'ummarta daga Ukraine inda suka tabbatar da cewar al'amura sun rincabe sai dai basu furta mamayar Rasha a kasar ba. An bukaci 'yan kasar China da 'yan Hong Kong gami da 'yan tsibirin Taiwan da su zauna a cikin shiri za a kwashe su nan ba da jimawa ba.

Yanzu haka sama da mutane 130 suka rasa rayukansu a Ukraine tun bayan da Rasha ta kutsa ciki.