China ta hanawa masu adawa da cinikaiyar duniya izinin shiga Hongkong | Labarai | DW | 04.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

China ta hanawa masu adawa da cinikaiyar duniya izinin shiga Hongkong

Mako daya gabanin fara babban taron cinikaiya ta duniya a Hongkong, hukumomin China sun haramtawa mutane 300 masu adawa da kungiyar cinikaiya ta duniya WTO shiga yankin. Kamar yadda jaridun China suka nunar, wannan haramcin ya fi shafar ´yan kasar KTK. Rahotanni sun nunar da cewa akalla mutane dubu 10 ake sa rai zasu je Hongkong din don yin zanga-zangar a lokacin babban taron na kungiyar ta WTO da zai gudana daga ranar 13 zuwa 18 ga wannan wata na desamba. Taron dai zai fi mayar da hankali ne akan batun sakarwar harkokin kasuwancin duniya mara. Don cimma wannan buri dai za´a kara matsawa tarayyar Turai lamba da ta kara rage kudin kwasta da take dorawa kayan amfanin gona da kuma rage tallafin da ta ke ba manomanta. To sai dai har yanzu EU ta ki ba da kai bori ya hau.