China ta bayyana shirin ci gaba da taimakon Siriya | Labarai | DW | 24.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

China ta bayyana shirin ci gaba da taimakon Siriya

China ta bukaci ganin an mutunta kudirin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dikin Duniya kan magance rikici tare bai wa Siriya makuden kudade.

Kasar China ta ce ta na shirye da bayar da taimakon da ya dace wajen warware rikicin kasar Siriya. Ministan harkokin wajen kasar ta China Wang Yi ya bayyana haka lokacin da yake karban bakuncin takwaransa na Siriya Walid Muallem, wanda yake ziyara a birnin Beijing. Ga abin da ministan harkokin wajen na China Wang ke cewa:

"Abu mai muhimmanci da muka amince shi ne magance rikicin siyasa a siyasance, kuma 'yan Siriya za su samar da mafita ga kansu karkashin saka ido na MDD. Kuma abubuwa da za a yi la'akari da su ke nan yayin tattaunawar kan Siriya."

Gwamnatin kasar ta China ta kuma bayyana bayar da taimako na kimanin dalar Amirka miliyan shida ga kasar ta Siriya mai fama da rikici.