1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China: Bude taron jam'iyyar kwamunisanci

Abdullahi Tanko Bala
October 18, 2017

Shugaban kasar China Xi Jinping ya kaddamar da babban taron jam'iyyar kwamunisanci ta kasar karo na 19 a birnin Beijin

https://p.dw.com/p/2m3Y4
China Peking Kommunistischer Parteitag Xi Jinping
Hoto: picture-alliance/AP Photo/N. Han Guan

Jam'iyyar kwamunisanci ta China a yau Laraba ta fara babban taronta na kasa karo na 19. 

A jawabinsa shugaban kasar Xi Jinping ya jinjinawa nasarorin da kasar ta samu a cikin shekaru biyar da suka wuce.

Ya bukaci 'yan jam'iyyar su kaucewa dukkan wani abu da zai tauye martabar kasar da kuma akidun da ta tsaya akan su.

Taron jam'iyyar wadda akan gudanar duk bayan shekaru biyar zai zabi sabbin shugabanni inda kuma ake sa ran Xi Jinpin zai sami wa'adin mulki karo na biyu na shekaru biyar a matsyin shugaba.

Wakilai fiye da 2000 ne ke halartar taron.