Charles Taylor ya ɗaukaka ƙara | Labarai | DW | 22.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Charles Taylor ya ɗaukaka ƙara

Wata kotun da a ka kafa a kan Saliyo da ke a birnin Hage za ta fara sauraran ɗaukaka ƙaran da tsohon shugaban Laberiya ya shigar don duba hukumcin da aka yanke masa

Tun farko dai kotun ta yanke wa tsohon shugaban hukumcin ɗaurin shekrun 50 na zaman gidan yari a cikin watan afirilu na shekara ta 2011

bayan da ta same shi da aikata laifukan yaƙi tsakanin shekaru 1996 zuwa 2002 .Tare kuma da bai wa yan tawayen Saliyio makamai su kuma suna ba shi lu'ulu'u a yaƙin basasar da kusan mutane dubu 120 suka mutu.Taylor ɗan shekaru 64 da haifuwa wanda ya yi mulki a Laberiya daga shekarun 1997 zuwa 2003 shine tsohon shugaba na farko da ya fuskanci hukmcin kotun bayan kotun da aka girka domin yin shari'a yan Nazi a yaƙin duniya na biyu.Ana sa ran charles Taylor ɗin dai zai halarci zaman kotun wacce lauyoyinsa zasu yi ƙokarin samun sasauci a kan hukumcin da aka yanke masa .

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Yahouza Sadissou Madobi