Chaina ta girke makamai masu linzami | Labarai | DW | 18.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chaina ta girke makamai masu linzami

Amirka ta bada sanarwar cewa Chaina ta girke makamai masu lizzami a tsibirin Woody wanda ake jayayya kansa tsakaninta da wasu kasashe makwabtanta

Dama tun a farkon wannan mako tashar talabijin ta Fox News ta Amirka ta ruwaito labarin da ke cewa Chaina ta girke wasu na'urori na harba makami mai linzami a tsibirin Woody.

Wani daga cikin manyan jami'an gwamnatin ta Amirka da bai bayyana sunansa ba ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa suna da hujjar cewa hotunan da aka wallafa na makami mai linzami ne sanfarin HQ-9 mai cin zangon kilomita 200.

Tuni dai sakataran harakokin wajen Amirka John Kerry ya yi tir da Allah wadai da matakin da Chainar ta dauka wanda ya ce zai mayar da hannun agogo baya ga kokarin da ake na neman hana barkewar tashin hankali a tsakanin kasashen yankin Asiya a tekun ta Chaina.