Chiana na bincike a duniyar wata
January 3, 2019Kamfanin dillancin labaran kasar ta Chaina, Chine Nouvelle ya ruwaito a wannan Alhamis cewa na'urar wacce aka harba daga doron kasa a ranar takwas ga watan Disamban da ya gabata ta yi nasarar sauka lami lafiya a yankin mai nisa na duniyar watan da misalin karfe 10 da mintoci 26 agogon Chaina wato karfe biyu da minti 26 agogon JMT.
Tashar talabijin ta CCTV ta kasar ta Chaina ta bayyana cewa tuni ma dai na'urar ta dauko hoton doron watan tare da aika shi ga taurarin dan Adam na Queqiao da ke hake a kewayen watan.
Wannan dai shi ne karo na farko da aka yi nasarar samun bayannai kan siffar fuskar wata da ke a boye da kuma ta kunshi manyan tudddai da ramuka sabanin bangaren da ke kallon duniya wanda ake da bayanai da dama kan abin da ya kunsa.
Na'urar da kasar ta Chaina ta yi nasarar aikawa a wannan sashe na wata za ta gudanar da bincike kan mitocin radiyo da arzikin ruwan da ya kunsa da kuma yiwuwar shuka tumatiri da sauran tsirrai.