1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

An sassauta dokokin corona a Chaina

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 1, 2022

Mahukuntan Chaina sun fara sassauta dokar kullen annobar corona, biyo bayan zanga-zangar da ta barke a manyan biranen kasar.

https://p.dw.com/p/4KMTw
Chaina | Yaki | COVID-19 | Dokoki | Zanga-Zanga | Shanghai
Bore da zanga-zanga a Chaina, kan dokoki yaki da annobar coronaHoto: REUTERS

Rahotanni sun nunar da cewa, an dage dokar kulle ta zuwa wani lokaci a birnin Guangzhou da ke zama cibiyar masana'antun kasar. Haka kuma an sassauta wasu ka'idojin yaki da annobar coronar, a wasu birane da suka hadar da Shanghai da Chongqing. Wannan matakin dai na zuwa ne, duk da karuwar wadanda suka kamu da cutar da ake samu a kasar. Zanga-zangar adawa da matakan kullen coronar dai, na zaman kin bin umurnin gwamnati mafi girma da aka gani a Beijing tun shekara ta 1989.