Chaina da Philiphines sun daidaita kan tsibirin Thomas Shoal
July 22, 2024Kasashen Chainada Philiphines sun sanar da cimma yarjejeniya don kawo karshen takaddama da suke yi a kan wani tsibiri dake kudancin tekun Chaina, ba tare da bayyana abin da aka cimma ba. Dukkan kasashen biyu na ikirarin mallakar tsibirin na Thomas Shoal wanda ke karkashin ikon fadar mulki ta Manilan a yanzu.
Karin bayani:Amurka da Pilippines na atisayen soji a tekun kudancin China
Philiphines ta kafa wani jirgin ruwa a shekarar 1999 domin sake nuna karfi da kuma ikonta akan tsibirin, ta kuma aike da wasu kananan jiragen ruwa a yankin. Sai dai Jiragen Chaina na amfani da wasu bututai masu fesa ruwa domin hana jiragen Philiphines samun damar zirga-zirga a yankin.
Karin bayani: EU na duba yiwuwar rage wa Chaina harajin shigar da motocinta Turai
An yi ta nuna damuwa kan karuwar zaman dar-dar a tsibirin da kuma yiwuwar tsoma bakin Amurka. Philippines ta na da dangantakar soji da Amurka kuma a na ganin za ta iya mara mata baya akan Chaina.