1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chaina da EU za su karfafa huldar kasuwanci

Yusuf Bala Nayaya
April 9, 2019

A wani sako na bai daya da suka fitar dukkanin bangarorin biyu sun amince da fadada ba da dama ta kasuwanci da kawar da tarnaki da ke sanyaya gwiwar masu zuba jari na kasashen ketare.

https://p.dw.com/p/3GWa8
Belgien EU-China Gipfel in Brüssel
Hoto: picture-alliance/AP Photo/O. Hoslet

Chaina da Kungiyar Tarayyar Turai sun amince da kara karfafa dangantaka ta kasuwanci tsakaninsu inda ma Chaina da ke zama kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya ta yi alkawarin samar da yanayi mai sauki da masu son zuba jari a kasar za su yi marhabun da shi don zuwa kasar.

A wani sako na bai daya da suka fitar dukkanin bangarorin biyu sun amince da fadada ba da dama ta kasuwanci da kawar da tarnaki da ke sanyaya gwiwar masu zuba jari na kasashen ketare.

Shugabanni daga EU Donald Tusk da Jean-Claude Juncker da Firaminista Li Keqian na Chaina sun bayyana batutuwa da dama a taron da suka kammala a Brussels, kafin daga bisani a bayyana wannan matsaya. Ga Chaina dai Tarayyar Turai ita ce babbar kawar kasuwancinta yayin da daga bangaren EU Chaina ke zama ta biyu bayan Amirka. Bangarorin biyu kan yi kasuwancin da ya kai Dala miliyan dubu 648 a shekara.