Chadi za ta shiga yaki da Boko Haram | Labarai | DW | 16.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chadi za ta shiga yaki da Boko Haram

Majalisar dokokin kasar Chadi ta kada kuri'ar amincewa da tura sojojin kasar zuwa Najeriya da Kamaru ba tare da hamayya ba, domin yakar kungiyar Boko Haram.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da shugaban kasar ta Chadi Idriss Deby Itno ya bayyana aniyarsa ta sanya hannu a yakin da ake da kungiyar ta masu tsattsauran ra'ayi. Kawo yanzu dai ba a bayyana adadin sojojin da Chadin za ta tura ba a wani yunkuri na hadin kai domin fatattakar kungiyar da ke neman zama annoba a yankin. A wani labarin kuma 'yan kungiyar ta Boko Haram sun tsare daruruwan mata da kananan yara a wata makaranta da ke garin Baga, garin da suka kai mummunan farmaki a farkon wannan wata na Janairu da muke ciki tare da hallaka mutane masu dimbin yawa. Rahotanni sun bayyana cewa wata mata da suka sako ce ta bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP inda ta ce akwai mata sama da 500 baya ga kananan yaran da kungiyar ta tsare a yanzu haka.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman