Chadi ta yi watsi da zargi kan Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 02.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chadi ta yi watsi da zargi kan Afirka ta Tsakiya

Ministan harkokin wajen Chadi Ahmat Mahamt Hassan ya sa kafa ta yi fatali da rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ya zargin sojojinta da aikata ba daidai ba a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

Gwamnatin Chadi ta yi watsi da rahoton bayan binciken da Majalisar Dinkin Duniya ta wallafa, inda ta zargin sojoji wannan kasa da aikata kisan-kiyashi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a shekara ta 2013 da kuma 2014. Cikin wata wasika da ya aika wa shugaban Hukumar Kare Hakkin bil Adama ta Duniya, ministan harkokin wajen Chadi Ahmat Mahamat Hassan ya zargi masu bincike da neman shafa wa sojojin kasarsa kashin kaji ,

Binciken da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar ya bada haske kan laifuffukan 620  ciki har da kashe-kashe da sojoji da 'yan tawayen suka aikata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tsakanin 2003 zuwa 2015, ciki har da dakarun Chadi.

Ita dai Majalisar Dinkin Duniya na son kafa Kotu ta Musamman da zata yi shari'ar laifukan yaki da aka aikata a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya. Sai dai Chadi da ta tura da dimbin sojoji wannan kasa ta yi barazanar katse hulda da wasu hukumomi na duniya idan aka tuhumi sojojinta.