1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi ta rufe iyakarta ta kasa da Libiya

Salissou Boukari
January 6, 2017

Hukumomin kasar Chadi sun sanar da rufe iyakarsu ta kasa da Libiya, inda suka ce akwai babbar barazana ta tsaro dangane da shigowar 'yan ta'adda cikin kasar domin tayar da hankali.

https://p.dw.com/p/2VP4a
Tschad Fahne Soldaten Kampf gegen Boko Haram Nigeria
Sojojin kasar Chadi bisa hanyarsu ta zuwa filin dagaHoto: Reuters/Emmanuel Braun

A cikin wani jawabi ne da ya yi ta kafofin yada labaran kasar, Firaministan kasar Chadi Albert Pahimi Padacket, ya sanar da wannan labari na rufe iyakar kasar da Libiya, inda ya ce dangane da babbar barazanar da ke fuskantar kasar ta Chadi gabaki dayanta, gwamnati ta dauki matakin rufe iyakarta ta kasa da kasar Libiya, sannan kuma dukannin yankunan na iyaka da kasar ta Libiya an kaddamar da ayyukan sojojin kasar ta Chadi a wani mataki na sa ido ga duk wata barazana da za ta iya kunno kai daga bangaran kasar ta Libiya.

Tschad Fahne Soldaten Kampf gegen Boko Haram Nigeria
Hoto: Reuters/Emmanuel Braun

Yankin Sahara na Tibesti da ke arewacin kasar ta Chadi, yanki ne dai da ke da karancin jama'a, amma kuma ya kasance inda al'ummomin bangarorin biyu ke gudanar da duk wasu muyagun ayyuka da suka hada da safara iri-iri. Matakan guda biyu dai da gwamnatin ta Chadi ta dauka, za su ba ta damar samar wa 'yan kasar cikeken tsaro da zaman lafiya. Sai dai Firaminista Pahimi Padacket ya ce tuni suka samu labarin wani gungu na 'yan ta'adda da ke shiri a yankin kudancin kasar Libiya, da ke zaman arewacin kasar ta Chadi domin kawo tadda zaune tsaye a Chadi, abun da ya ce ba za su yadda da shi ba.

Tschad Pressekonferenz von Präsident Deby
Shugaban Chadi Idriss Deby a shekara ta 2008Hoto: AP

A ranar 12 ga watan Disamba ne dai wani gungu na 'yan tawayen kasar ta Chadi, na FACT "Front pour l'alternance et la concorde au Tchad" ya sanar cewa, wasu jiragen yaki da ke karkashin ikon Marshal Khalifa Haftar shugaban wani bangare da sojojin kasar Libiya sun kai musu hari, inda suke zargin Haftar din da gama baki da Shugaba Idriss Deby na Chadi. A farkon watan Afirilu ne dai da ya gabata, aka sanar da kafuwar kungiyar 'yan tawayen ta FACT, ake a matsayin wani reshe na tsofuwar kungiyar UFDD ta sananan dan tawayen nan na kasar ta Chadi Janar Mahatma Souri wadda ta kai wani samame har ya zuwa birnin Ndjamena a watan Febrairu na 2008 da zimmar kifar da gwamnatin Shugaba Idriss Deby kafin daga bisani sojojin kasar su kore su.