Chadi ta ce tana cikin zaman mummunar gaba da Sudan | Labarai | DW | 24.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chadi ta ce tana cikin zaman mummunar gaba da Sudan

Gwamnatin Chadi ta ce tana cikin wani hali na yaki da makwabciyarta Sudan. An ba da wannan sanarwa ce bayan da shugaban Chadi Idriss Deby ya zargi takwaransa na Sudan da shirya wata makarkashiyar ta da zaune tsaye a cikin kasar sa, bayan wani harin da aka kai kan garin Adre na kan iyaka yayi sanadiyar mutuwar mutane 100 a karshen makon jiya. Gwamnatin Chadi ta ce gwamnatin Khartoum na da hannu a wannan hari. Sudan dai ba ta dade ba da fita daga wani yakin basasa da aka kwashe shekaru 20 ana yi tsakanin gwamnatin tsakiya a birnin Khartoum da ´yan tawayen kudancin kasar. To amma a lardin Darfur dake yammacin kasar kuma ke da iyaka da Chadi, har yanzu ana fama da rikicin ´yan tawaye dake fafatukar neman ´yancin cin gashin kai. Mutane kimanin miliyan daya da rabi sun tsere daga gidajensu yayin da aka halaka dubbai a wannan yanki.