Chadi ta ce ba ta da hannu a rikicin Afirka Ta Tsakiya | Labarai | DW | 04.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chadi ta ce ba ta da hannu a rikicin Afirka Ta Tsakiya

Gwamnatin Chadi ta yi watsi da zargin nuna goyon bayanta ga 'yan tawayen Seleka.

BANGUI, March 31, 2013 (Xinhua) -- Central African Republic's self-proclaimed President Michel Djotodia (L) attends a rally in Bangui, capital of Central African Republic, on March 30, 2013. Djotodia said he would not take reprisals against rivals and called on those who fled abroad to return on the Saturday rally. (Xinhua/Thierry Messongo) (jl) XINHUA /LANDOV

Zentralafrikanische Republik Michel Djotodia

Gwamnatin kasar Chadi ta yi watsi - da kakkausar lafazi dangane da zarge zargen da hambararren shugaban jamhuriyyar Afirka Ta Tsakiya Francoir Bozize yayi na cewar, ta taimakawa kungiyar 'yan tawayen Seleka, wadanda suka kifar da gwamnatinsa kimanin kwanaki 10 da suka gabata. A cikin wata sanarwar da gwamnatin kasar ta Chadi ta fitar a wannan Alhamis (04.04.2013), ta ambata cewar: Tsohon shugaba Bozize ya gabatar da muhimman zarge zargen da gwamnatin Chadi ke yin watsi da su domin kuwa babu wani kamshin gaskiya a cikinsu.

Idan za ku iya tunawa dai tsohon shugaban jamhuriyyar Afirka Ta Tsakiya Farancoir Bozize ya nemi mafaka a jamhuriyyar Kamaru da ke makwabtaka da kasarsa, bayan kifar da gwamnatinsa, inda a wani taron sHugabannin yankin daya gudana a kasar Chadi a wannan Larabar (03.04.2013), shugaba Idris Deby na kasar Chadi ya bukaci jamhuriyyar Bini ta baiwa tsohon shugaba Bozize mafakar siyasa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman