1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi na buƙatar agajin ƙasashen duniya saboda sojojinta a Mali

April 17, 2013

Gwamnatin ta ce a cikin watanni uku kawai na yaƙi da sojojinta suke yi a arewacin Mali da masu kishin addinin, ta kashe miliyoyin daloli wajen ɗaukar nauyin sojojin.

https://p.dw.com/p/18HQj
Chadian President Idriss Deby Itno speaks to the press after meeting with French President Nicolas Sarkozy at Elysee Palace in Paris, France, 19 July 2007. Mr. Sarkozy received Idriss Deby Itno, who is on an official visit to France. Foto: EPA/HORACIO VILLALOBOS +++(c) dpa - Report+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Kimanin biliyan 57 na kuɗi CFA ,daidai da miliyan 87 na kuɗin Euro hukumomin ƙasar ta Chadi suka ce sun kashe a cikin watanni 90 domin ɗaukar ɗawainiyar sojojin na su. Kuma Fira ministan ƙasar ya ce idan dai ƙasashen duniyar ba su kawo musu ɗauki ba, to a cikin shekara guda gwamnatin za ta kashe sama da biliyan 90 domin kula da sojojin.

Kiran gwamnatin ga ƙasahen duniya akan buƙatar

Wannan furci dai na zuwa ne kwanaki ƙadan bayan da 'yan majalisar dokoki na ƙasar suka kaɗa ƙuri'a janye sojoji na Chadi daga Mali da sannu a hankali. Adadin sojojin na Chadi a Mali ya kai 2250. Kawo yanzu dai an hallaka sojojin na su 36 yayin da wasu 74 suka samu raunika. Yawan kudaɗen da ƙasar ta kashe akan harkokin sojin ya fara janyo tsokacin al'ummar ƙasar da ke fama da rashi da kuma talauci. Francois Djondang shi ne babban sakatare na haɗaɗiyar ƙungiyar ƙwadago na kasar.

Chadian soldiers form a line with their armoured vehicles in the northeastern town of Kidal, Mali, February 7, 2013. Around 1,000 troops from Chad led by the president's son advanced towards the mountains of northeast Mali on Thursday to join French search-and-destroy operations hunting Islamist jihadists. Picture taken February 7, 2013. REUTERS/Cheick Diouara (MALI - Tags: POLITICS CIVIL UNREST CONFLICT)
Sojojin Tcha a MaliHoto: Reuters

Ya ce: ''ya ce akan wannan batu lokaci ya ba mu gaskiya, da farrko hukumomin sun ce suna da kuɗaɗen yin aiki,amma sai ga shi haka ta faru.Tun da farko mun amince da tura sojojin mu zuwa Mali amma abinda daman ba mu amince da shi ba, shi ne yadda yawan sojojin mu ya zarta na ɗaukacin sojojin ƙasashen yammancin Afirka da suka shiga faɗan.''

Faransa dai ta shawarci kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya da ya amince da wani ƙudirin, da zai ba da damar soma gudanar da aikin rundunar kiyaye zaman lafiya ta majalisar daga bakin ranar ɗaya ga watan Yuli wato MINUSMA. Wace za ta ƙunshi yawan dakaru dubu goma sha ɗaya da yan sanda 1440 don maye gurbin rundunar dakarun kiyaye zaman lafiya ta Afirka MISMA. Kuma MDD na buƙatar samun tallafin sojoji na Chadi.

Koken jama'a na halin tsadar rayuwa a ƙasar ta Tchad

Tun da farko dai shugaba Idriss Deby ya sanar da cewar yaƙin gaba da gaba tare da yan ta'addar ya ƙare don haka zai janye sojojinsa, saboda ya ce ba su da ƙorewa akan yaƙin sankuru, to amma ya ce idan MDD ta ɓukaci samun tallafinsu ya ce dole ne su bayar. To sai dai da allama za a samu rashin yarda al'umma ta ƙasar da ke fuskantar halin tsadar rayuwa Sakataren ƙungiyar ƙwadagon ya ƙara da cewar.

Gemüseverkäuferin an ihrem Stand auf dem Markt in Abéché, Region Ouaddaї. Copyright: Albrecht Harder 19.11.2011, Abéché
Masu sayar da kayan lambu a TchadHoto: Albrecht Harder

Ya ce:'' Inda gwamnatin ba za ta ɗauki matakin rage tsadar rayuwa ba na kayan abicin a bisa kasuwanni, jama'a za su ɗanɗana kuɗar su.''

Wannan al'amari dai na daf da zubar da farin jini da martabar da shugaban ƙasar ya ke da ita, wanda tuni har 'yan jam'iyyar da ke yin mulki suka fara nuna damuwa a kan abinda suka kira zakara ba da ayya ka tauna tsakuwa.

Daga ƙasa za a iya sauraran wannan rahoto da kuma rahoton da wakilinmu Mahaman Kanta ya aiko mana daga Nijar dangane da muhawara da al'ummar ƙasar ke yi akan ci-gaba da kasancewar sojojin ƙasar a Mali

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi