Chadi: Majalisa ta amince da tswaita wa′adin Deby | Labarai | DW | 30.04.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chadi: Majalisa ta amince da tswaita wa'adin Deby

Duk da cewa 'yan adawa sun kaurace lokacin kuri'ar tabbatar da dokar, amma bakin alkalami ya bushe inda sabuwar dokar za ta bai wa Shugaba Idriss Deby damar sake takara bayan zaben shekarar 2021.

'Yan majalisar dokokin kasar Chadi, sun rattaba hannu kan kudurin dokar da ke neman yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, dokar dai za ta bai wa shugaba Idriss Deby damar tsawaita wa'adin shugabancinsa har zuwa shekara ta 2033.

A yanzu dai tuni majalisar dokoki ta mika dokar ga shugaban kasa saboda ya saka hannu kafin haka ya zama tabbataciyar doka.