1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi: Gwamnati ta yi sulhu da 'yan kwadago

Dariustone Blaise SB
March 15, 2018

Gwamnatin Chadi da kungiyoyin kwadago sun cimma yarjejeniya a game da yajin aikin da ma'aikata suke yi. Sai dai kuma ana ganin cewar cimma yarjejeniyar ba yana nufin kawo karshen yajin aikin da ma'aikatan suke yi ba.

https://p.dw.com/p/2uNj4
Tschad Demonstrationen
Hoto: DW/D. Blaise

Sai bayan da aka shafe awowi fiye da bakwai ne ana tattaunawa tsakanin gwamnatin ta Chadi da kungiyoyin kasar ne aka samu kai ga cimma wannan yarjejeniya a karkashin shiga tsakani na shuagaban kasar ta Chadi driss Déby Itno da ya yi alkawarin kiyaye hanyoyin aiwatar da wannan yarjejeniya. Michel Barka shugaban hadin gwiwar kungiyoyin kwadagon da suka yi yajin aikin ya ce ya na tsammanin sun samu abin da suke bukata.

Tun dai sanar da sakamakon wannan yarjejeniya a ranar Laraba, al'ummar kasar ta soma tofa na ta albarkacin baki musamman ma ta kafofin sadarwa na zamani, inda wasu ke ganin cewar gwamnatin na iya yaudarar kungiyoyin kwadagon wanda wasu ke ganin cewar wannan yarjejeniya ba ta nuna kawo karshen sassare albashin da ake yi na ma'aikatan ba wanda kuma hakan shi ne ya haifar da yaje-yajen ayyuka a kasar ta Chadi.

Tschad Proteste in Ndjamena
Hoto: DW/F. Quenum

Yarjejeniyar dai ta tanadi dakatar da yajin aikin 'yan kwadagon tare da komawa ga bakin aiki bayan biyan dukannin albashin ma'aikatan sannan da kuma ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin don ganin an samar da zaman lafiya da yanayi na aiki a kasar. Burin da gwamnatin ta Chadi dai ta sama gaba, shi ne na rage samun ragowar kudade har miliyan dubu 30 na CFA daga kudaden albashin da take biya a ko wane wata.