1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Chadi ta rage karfin Intanet a kasar

Gazali Abdou Tasawa MNA
August 4, 2020

Gwamnatin Chadi ta sanar da rage karfin Intanet a kasar domin rage yaduwar sakonnin kyamar juna da ke mamaye shafukan sada zumunta a kasar a baya baya nan.

https://p.dw.com/p/3gNTC
Social Media-Nutzung in Afrika
Hoto: AFP/Getty Images/I. Sanogo

Gwamnatin Chadi ta sanar da rage karfin Intanet a kasar domin rage yaduwar sakonnin kyamar juna da ke mamaye shafukan sada zumunta a kasar a baya baya nan, matakin da ministan sadarwa kana kakakin gwamnatin Chadi, Mahamat Zene Cheriff ya ce ya soma aiki ne tun a ranar 22 ga watan Yulin da ya gabata, amma za a dage shi nan ba da jimawa ba.

Sai dai wasu daga cikin shugabannin kamfanonin waya na kasar da suka bukaci a sakaya sunayensu sun ce matakin na da alaka ne da wani faifayen bidiyo da ke yawo inda wani babban jami'in sojin kasar ya buda wuta da bindiga kan wasu masu aikin kanikanci su biyu wadanda su kuma suka kai masa hari da wukake a lokacin wata rigima da ta barke a tsakaninsu a ranar 14 ga watan na Yuli.

Hukumomin shari'ar kasar sun sanar da cewa daya daga cikin mutanen da sojin ya harba ya rasu a yayin da shi sojin wanda aka kwatar da shi bayan ya ji rauni a cikin fadan zai gurfana a gaban kuliya.