Cece-kuce kan zaben ‘yan majalisa a Chadi | Siyasa | DW | 14.11.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Cece-kuce kan zaben ‘yan majalisa a Chadi

Sake dage zaben 'yan majalisar dokoki ba zato ba tsammani da gwamnati ta yi ya jawo cece-kuce tsakanin al'umma da 'yar siyasan kasar sai dai gwamnatin tace rashin kudi ne ya dage zaben.

Tun a ranar 21 ga Yuli na shekarar 2015 ne ya kamata wa'adin 'yan majalisa da ke ci yanzu ya kare. Amma shugaban kasar Idriss Deby Itno ya yi amfani da karfin ikon da kundin tsarin mulki ya bashi wajen tsawaita shi har sai abin da hali yayi. Sai dai daga bisani an tsayar da wannan watan Nuwamba a matsayin lokacin gudanar da zaben na 'yan majalisa, kafin rashin masu gida rana ya sa a sake dage shi zuwa watan Mayu na shekara mai zuwa.

A cewar shugaban kasar Chadin, Idriss Deby Itno, shirya wannan zabe zai lakume kudi da ya kai miliyan dubu 70 na CFA, kimanin miliyan 100 na Euro, alhali kasar na fama da matsin tattalin arziki. Wannan dalilin ne ya sa shugaban kasar yin kira ga abokan hulda na kasashe masu hannu da shuni don taimaka wa kasarsa shirya zabbuka na gaba.

Amma ga wasu daga cikin masu jefa kuri'a na Chadi sun fara kosawa da dage zaben 'yan majalisar da gwamnatin ta yi har sau biyu a cikin shekaru ukun da suka gabata, suna masu cewa wannan lamari ya saba wa dimukaradiyya.

Amma kuma 'yan adawa sun nesanta kansu daga zargin hada baki da shugaba Deby Itno wajen dage zaben.

Wannan ba shi ne karon farko da ake tsawaita wa 'yan majalisar dokokin Chadi wa'adi ba. A farkon shekarun 2000 ma sun shafe shekaru takwas daga 2003 zuwa 2011 kafin a gudanar da sabon zabe.

Sauti da bidiyo akan labarin