Cece-kuce kan dokar kada kuri′a a Najeriya | Siyasa | DW | 26.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Cece-kuce kan dokar kada kuri'a a Najeriya

Hukumar zaben Najeriya ta INEC na neman dokar da za ta amince wa 'yan Najeriya da ke zama a wajen kasar su kada kuri'a.

Wahlen Nigeria Attahiru Jega

Attahiru Jega, Shugaban INEC

Ta dai kira sunan sauyi ta kuma ce a fadada, ga hukumar zaben Tarayyar Najeriya ta INEC, da ta ce tana shirin tsawaita tsarin zabukanta, tare da bada dama ga 'yan kasar da ke waje su samu damar zabe tun daga zabukan shekara ta 2015.

Tuni dai hukumar ta mikawa majalisun Tarayyar kasar biyu, bukatar gyaran sashi na 77 na kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya tanadi yin rijista dama zabuka a unguwannin kowa, domin kafa dan ba ta samar da damar zabukan ga miliyoyin 'yan kasar da ke waje na taka rawa wajen fitar da shugabanninsu tun daga zabe mai zuwa.

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria

Majalisar dokokin Najeriya

Kama daga Sudan mai miliyan kusan 12 ya zuwa Amirka da ke takama da yan kasar ta Najeriya kusan miliyan biyar da ragowar kasashen yankin yammacin Afirka, da adadi mai tsokar al'ummarsu ke zaman daga Najeiyar. Akalla 'yan kasar tsakanin miliyan 30 zuwa 40 ne dai ke warwatse wajen kasar, a sassa daban-daban na duniya da hukumar INEC ke fatan taka rawar su na iya kyautata tsarin zabe, dama tabbatar da yancin kowa a kasar, a fadar Nick Dazang da ke zaman kakakin hukumar zaben ta kasa.

To sai dai kuma tun ba a kai ga ko'ina ba, fatan INEC din ke shirin fuskantar tasku tsakanin 'yan siyasar kasar, dama masu shirin dokar da ke masa kallon da biyu, wadanda kuma suka ce bakin rai bakin fata ga adawarsu da sabon yunkurin da ke fuskantar fassara iri-iri.

Ana dai kallon gazawar INEC din a zaben gwamnan jihar Anambra dama ragowar zabukan da ke can baya, a matsayin zakaran gwajin dafin tunanin 'yan dokar da ke da alhakin amincewa da bukatar gyaran. Wadanda kuma suke karatun da walakin, a fadar Hon Ahmed Babba Kaita da ke zaman dan majalisar wakilan kasar daga Katsina.

Kokarin yaki da murdiyar INEC ko kuma tabbatar da yanci na 'yan Najeriya da ke zama a waje dai, ko bayan nan ma dai a tunanin masu adawar kasar ta Najeriya, har ya zuwa yanzu su kansu ofisoshi na jakadancin kasar da ke waje, da kuma ke zaman cibiya ta tattara kuri'un na da kama da 'yan amshin shatar PDP mai mulki ne. A fadar Engineer Buba Galadima da ke zaman jigo a jam'iyyar APC ta adawa.

Abun jira a gani dai na zaman dabara ta gaba, a cikin hukumar da ke fatan gina sabon babi na zabukan cikin kasar da har ya zuwa yanzu, karbabbun zabuka ke kama da mafarkin safe.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin