Cece-kuce kan aikin gina hanyar mota a Cross River | Zamantakewa | DW | 19.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Cece-kuce kan aikin gina hanyar mota a Cross River

Gwamnatin jahar Cross River ta dau aniyar aiwatar da aikin gina katafariyar hanyar motar nan mai tituna shida zuwa goma a hagu da dama, amma mazauna garuruwan da aikin zai bi na nuna adawa da shirin.

Gwamnatin jahar Cross River ta dau aniyar aiwatar da aikin gina katafariyar hanyar motar nan mai tituna shida zuwa goma a hagu da dama. Sai dai kuma kungiyoyi da kuma al'ummomin da aikin gina hanyar zai bi ta garuruwansu suna nuna kin amincewarsu da wannan hanya a sakamkon albarkatun gandun daji da za a kassara da kuma gonaki. Gwamnan jahar Cross River ya ce wannan aiki ba gudu ba ja da baya, domin dukkanin masu adawa da aikin wannan hanya 'yan haifar da nakasu ne kawai a harkokin ci gaban Kasa.


Batun gina wannan katafariyar hanya dai mai tsawon kilomita 260, da kuma ke da fadin mita dari biyu,da ko wane hannun zai dau kimanin tituna goma ya fara ne da shan suka daga al'ummomin garuruwa kimanin 100 da kungiyoyin kare muhalli da dama, a bisa hujjar cewar aikin bai yi la'akkari da asarar gandun daji da tsirrai da gonaki da za a yi ba. Kan haka ma dai sai da al'ummi ta shigar da karar gwamnatin jahar Cross River a yankin Niger Delta da ita ce ta tashi haikan don aiwatar da wannan aikin hanya, da zai ci kudi kimanin Naira biliyan dari bakwai.
Kuma yau kimanin shekara daya kenan da kaddamar da fara wannan aikin hanya da shugaban Najeriya ya yi a Jahar ta Cross River, amma daga bisani dole aka dakatar da shi a sakamakon takaddamar da ta ki ci ta ki cinyewa. Gwamnan Jahar ta Cross River Farfesa Ben Ayade ya tabbatar da cewar aikin hanyar yana nan daram .

 

"Da farko dai ina son tabbatar maka babu wani haufi da zai hana gina wannan hanya, kuma batun hukuncin kwararru kan muhalli dangane da aikin, abu ne da an riga an gama shi ba tare da matsala ba, illa dai kawai wadanda ba sa nufin Jahar Cross River da alhairi na ci gaba da yada farfagandar karya cewar aikin hanyar ba zai yiwu ba, kuma muna da shirin gwamnati na dasa bishiyoyi kimanin miliyan biyar nan gaba da ma za su dara yawan na gandun dajin da ake ta magana wannan hanya za ta barnata, kuma dai magana yanzu ita ce an riga an warware dukkanin wata takaddama don fara wannan aiki."

Tuni dai gwamnatin ta gayyato wani kamfanin kasar Chaina da ke da sha'awar kwangilar gina wannan hanya don duba yiwuwar fara gina ta kamar dai yadda Mr Tanglang shugaban wani Kamfanin na China ya yi karin bayani:


"Mun zo jahar Cross River da ke Najeriya, kasar da ta dara ko ina a Afirka, kuma zance kamfanimmu ya yi sa'a ta karbar wannan aiki, kuma da fatan za mu kai ga nasarar fara wannan aiki."

Wani direban mota da ke son ganin wannan aikin hanya ta Super Highway ya kankama, inda ma har yake tsokacin cewar daukacin takaddamar da ke bibiyar aikin ta siyasa ce.

Ga dukkanin alamu dai bisa tuntubar wasu bangarori da na yi, da kuma ke kan aniyarsu ta kare muhalli, da kuma ba su yarda sun bayyana muryarsu ba a sakamakon cewar sun kai kara kotu, na ganin har yanzu tsugune ba ta kare ba.