1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsawaita wa'adin yan majalisar dokoki a Gini

Abdoulaye Mamane Amadou
January 18, 2019

Shugaba Alpha Conde na kasar Gini ya kara wa’adin ‘yan majalisar dokokin kasar wanda a ka’ida ya kawo karshe a ranar 13 ga wannan janairu. Sai dai matakin ya janyo cece-kuce.

https://p.dw.com/p/3Bo1l
Alpha Conde
Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Shugaba Alpha Conde na kasar Gini ya kara tsawaita wa’adin ‘yan majalisar dokokin kasar, da a ka’idance ya kawo karshe tun a ranar 13 ga wannan watan na janairu. To sai dai matakin baiwa ‘yan majalisun dokokin damar zarcewa har zuwa shekarar 2020, ya janyo cece-kuce musamman daga bangarorin siyasa da kungiyoyin rajin kare dimukuradiyya.

A ranar 13 ga watan Janairun 2014 ne dai ‘yan majalisun dokokin kasar Gini suka karbi rantsuwar kama aiki gadan-gadan, a wani wa’adin na shekaru 5 na wakilcin al’ummar kasar, sai dai a yayin da wa’adin majalisar dokokin ke kawo karshe ba tare da gudanar da zabe ba, ba zato ba tsammani shugaban kasar Alpha Condé, ya dauki matakin tsawaita wa’adin ‘yan majalisar har zuwa wani lokacin da za a gudanar da sabon zabe, bisa hurumi na tuntubar kotun tsarin mulkin kasar.

Tuni dai matakin ya janyo zazafar mahawara. Daouda David Camara dan majalisar dokokin kasar ta Gini ne.

Guinea Bissau 1. Parlamantssitzung nach Krise
Wakilan majalisar dokokin kasar GiniHoto: DW/B. Darame

"Majalisar dokoki ta kasa, ai ba ita take tsara zabe ba, da akwai hukuma ta musamman da ke da kwarewa a kai mai suna Ceni, za mu tafi wannan zaben a duk lokacin da hukumar ta yi yekuwar kiranmu."

Duk da yake wasu ‘yan majalisun dokokin sun nuna amincewa da matakin shugaba Conde, ga Ousmane Kaba dake matsayin shugaban wata jam’iyyar siyasa kuma dan majalisar dokoki, cewa ya yi shi kam a kai kasuwa.

"Al’ummar Gini ta bamu wa’adin shekaru biyar ne kawai  kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, to amma haka kawai sai a zo a dauki wani mataki na shugaban kasa don kara wa’adin ‘yan majalisa?, wannan ko kadan bai yi ba domin ya sabawa ka’ida".

Suma dai kungiyoyin rajin kare Dimukradiyya nuna rashin gamsuwa suka yi da matakin kara wa’adin na ‘yan majalisar dokokin tare da bayyana matakin matsin lamba ga gwamnati har sai ta gudanar da zabubbuka a kasar a cikin takaitacen lokaci. Tun a shekara ta 2000 ne dai kasar ta Gini ke fuskantar irin wannan matsalar ta karin wa’adi, inda daukacin majalisun dokokin da suka gabata ke zarta wa‘adinsu na kundin tsarin mulki.