Canjin sheƙa na ′yan siyasa a Najeriya | Siyasa | DW | 30.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Canjin sheƙa na 'yan siyasa a Najeriya

Lamarin na canjin sheƙa a Najeriya na ɗaukar wani mugun salo tun bayan da ɗaya daga cikin shugabannin jam'iyyar APC Malam Ibrahim Shekarau ya koma PDP.

Shakka babu jama'ar ƙasar na lura sau da kafa halin da lamarin siyasar na Najeriya yake cike, wanda bayan canji sheƙa na Shekarau ɗin, wasu 'yan majalisun dattawa guda 11 tare dawasu gwamnonin jihohi uku suma suka canza sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai adawa daga jam'iyyar PDP mai mulki.

Sabbabin masu sauyin sheƙar dai sun haɗa da tsoffafin gwamnonin jam'iyyar PDP uku, Sanata Bukola Saraki, da Sanata Danjuma Goje da kuma Sanata Abdullahi Adamu.
Sauran sun haɗa da sanata Ali Ndume daga Borno, da Sanata A'isha Jumai Alhassan daga Taraba da dai sauransu.

DW.COM