1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cameron na ziyara a Afghanistan

Yusuf BalaOctober 3, 2014

Firaministan na Birtaniya na zama na farko da ya ziyarci Afghanistan daga cikin shugabannin yammacin duniya bayan da Ashraf Ghani ya zama shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/1DPIq
Großbritannien Parteitag Conservative Party David Cameron 01.10.2014
Hoto: Reuters/Luke MacGregor

A wata ziyara da ba a bayyana ba tun da fari zuwa kasar Afghanistan a ranar Juma'annan Firaminista Cameron ya isa kasar dan ganawa da shugabannin gwamnatin hadakar kasar. Shugaba na farko cikin jerin jigon shugabanin kasashen yamma da ya ziyarci wannan kasa tun bayan samar da mafita kan rikicin siyasar kasar, abinda ya hana sake afkawarta cikin mummunan rikici.

Wannan ziyara ta sa na zuwa ne kwanaki hudu bayan rantsar da shugaba Ashraf Ghani wanda ya kama aiki bayan wasu watanni na rudanin siyasa da kasar ta shiga.

Bayan dai kwashe takaddama tun bayan kada kuri'a zagaye na biyu tsakanin Ashraf Ghani da abokin karawarsa Abdullah Abdullah a watan Yuni, kafa gwamnatin gambizar dai na zama mafita ga rikicin siyasar kasar.

Amurka da Birtaniya kuma na zama manyan kasashe da su ke da sojoji mafiya yawa cikin sojan kawance da suke tallafa wa wannan kasa ta Afghanistan tun bayan kifar da gwanmnatin masu tsatstsauran ra'ayi a shekarar 2001 bayan harin 11 ga watan Satimba a Amurka.