CAF: Mohamed Salah yafi iya taka leda a Afirka | Labarai | DW | 05.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

CAF: Mohamed Salah yafi iya taka leda a Afirka

Nasarar Salah dan wasan gaba a kungiyar kwallon kafr Masar a matsayin gwarzon kwallon kafa a Afirka na zuwa ne yayin da a bangare guda ya fara jan zarensa a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool.

Ghana Fußballer Mohamed Salah in Accra (Getty Images/AFP/U. Ekpei)

Mohamed Salah a (dama) gwarzon kwallon kafar Afirka na 2017

An zabi Mohamed Salah a matsayin dan wasa da yafi iya murza leda a Afirka a shekarar 2017. Salah dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafar Masar ya samu wannan nasara bayan jan ragama da ya yi a fafutikar ganin kasarsa ta Masar ta kai ga zuwa wasan kwallon kafa na duniya da za a yi a Rasha, wasan da ta dade tana fatan zuwa. Yayin da a bangare guda ya fara jan zarensa a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool.

Lambar yabon ta CAF da aka bayar ga Salah a bikin da aka yi ranar Alhamis a kasar Ghana na zuwa ne bayan takara da takwaransa Sadio Mane dan Senegal da ya zo na biyu da Pierre-Emerick Aubameyang dan Gabon da ke taka leda a kulob din Borussia Dortmund a nan Jamus na uku.

Salah dai ya ce wannan abin farinciki ne a gare shi: "Tabbas na yi farin ciki da samun wannan lambar girmamawa, ina alfahari da ita, karon farko da na samu, ina cikin farinciki tare da abokina (Sadio Mane) wanda nan ba da dadewa ba ne nake fatan zai samu wannan lambar girmamawa."