Côte d′Ivoire ta mika Blé Goudé ga ICC | Labarai | DW | 22.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Côte d'Ivoire ta mika Blé Goudé ga ICC

Blé Goudé ya kasance jagoran matasa 'yan gani kashenin tsohon shugaba Laurent Gbagbo, wanda ake zargi da laifin kissa a rikicin da ya biyo bayan zaben 2010

Yau ne hukumomin kasar Côte d'Ivoire suka mika Charles Blé Goudé, ga hannun kotun duniya ta hukunta manyan laifukan yaki ta kasa da kasa, wato ICC dake birnin The Hague na kasar Holland, inda ake zargin sa da laifin kissan al'umma a wannan kasa.

Wannan labari ya fito na daga gwamnatin kasar ta Côte d'Ivoire kuma kotun duniyar da kanta ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa.

Da yake bayani wa kanfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP, kakakin gwamnatin wannan kasa Affoussiata Bamba ya ce, tuni dai jirgin da kotun ta samar domin jigilar wannan fursuna na ta, ya tashi daga Abijan babban birnin kasar ta Côte d'Ivoire, a wannan Asabar din, inda ake sa ran saukar sa a birnin The Hague inda cibiyar wannan kotu take.

Shi dai wanda ake tuhumar M. Blé Goudé dan shekaru 42 da haihuwa, ya kasance jagoran matasa 'yan gani kashenin dake marawa Laurent Gbagbo baya a lokacin mulkin sa, kuma an kama shi ne a watan Janairu na shekarar 2013 a kasar Ghana, bayan da ya tsere kuma ya buya a wannan kasa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Pinado Abdu Waba