Bush ya lashi takobin yaki da kwararowar bakin haure | Labarai | DW | 29.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bush ya lashi takobin yaki da kwararowar bakin haure

Shugaban Amurka George W Bush na rangadin jihohin kasar domin samun goyon baya ta tsaurara matakan shige da fice. Shugaban na bukatar kara daukar matakan tsaro a kan iyakokin Mexico. A karkashin tanadin dokar da yake shirin gabatarwa zaá baiwa baki yan cirani wadanda suka sami aiki a kasar izinin zama amma ba na dundundun ba, bakin haure kuma wadanda basu da cikakun takardun zama, zaá basu Visa ta shekaru uku ne kawai domin yin aiki. Wasu yan jamíyar Republican sun soki lamirin shawarar da cewa tamkar wata tukwici ce ga bakin haure. A nasa bangaren Bush yace shirin zai rage kwararowar mutane dake shigowa ta kan iyakoki ba bisa kaída ba, domin aikin kwadago sannan zai saukakawa jamián tsaro waje kame bata gari da masu safarar miyagun kwayoyi da kuma yan taádda.