Burundi: Kammala kidayar masu zabe | Labarai | DW | 20.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Burundi: Kammala kidayar masu zabe

Hukumar zaben Burundi ta sanar cewa, fiye da mutane miliyan biyar ne aka kidaya a jerin sunayen masu zabe a shirin da kasar ke yi na zaben rabagardama, wanda zai kawo sauyi ga kundin tsarin mulki.

Shugaban hukumar zaben kasar Pierre-Claver Ndayicariye, ya sanar da wannan labari a wannanTalatar bayan da aka kammala kidayar jama'ar a ranar Asabar da ta gabata. A cewar gwamnatin ta Burundi fitar da jama'a suka yi domin a kidayasu, ya nunar da yadda suka nuna kishin kasa a fili ganin cewar da farko hukumar zaben ta ce ba ta tsammanin samun mutun miliyan hudu da rabi da za su rububa sunayansu a kundin zaben sai gashi adadin ya fice haka.

Da farko dai kafofin yada labaran kasar ta Burundi sun sanar cewa mutane basa fita sosai domin kidayar. Zaben rabagardaman da zai gudana a watan Mayu mai zuwa zai iya bai wa Shugaba Pierre Nkurunziza damar tsayawa a kan mulki har ya zuwa shekara ta 2034.