Burundi: Harin roka kusa da fadar shugaban kasa | Labarai | DW | 19.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Burundi: Harin roka kusa da fadar shugaban kasa

Harsashen roka biyu sun fado a unguwar Kiriri kusa da fadar Shugaba Nkurunziza a daren jiya Laraba ba tare da haddasa asarar rai ko ta wata kadara ba.

Rahotanni daga kasar Burundi na cewar an harbo wasu harsasan roka guda biyu a daran jiya a gaban fadar shugaban kasar da ke a birnin Bujumbura. Kamfanin dillancin labaran Faransa wanda ya ruwaito labarin da ya ce wani jakadan wata kasar Turai da bai so a bayyana sunansa ba ne ya kwarmata mata shi, yu nunar da cewar an harbo makaman ne daga saman tsaunikan da ke kewaye da birnin na Bujumbura.

Amma makaman sun tarwatse a unguwar Kiriri ta kusa da fadar shugaban kasar ba tare da haddasa asarar rai ko ta wata kadara ba. Tuni kuma wata majiya ta gungun mutanen da ke yakar milkin shugaba Nkurunziza da makamai ta dauki alhakin kai wannan hari.Sai dai kakakin hukumar 'yan sandar Shugaban Pierre Nkurunziza ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewar labarin harin ba gaskiyya ba ne domin sun gudanar da bincike a gurin da aka ce an harbo makaman ,amma babu abin da suka iske.