Burundi: AU za ta aike da sojoji | Labarai | DW | 28.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Burundi: AU za ta aike da sojoji

A wannan makon da muke ciki ne shugabanin Afrika zasu kada kuri'ar amincewa da batun aikewa da tawagar sojojin kungiyar AU dubu biyar zuwa Burundi .

Aikewa da rundunar sojojin Kungiyar tarayyar Afrikan na zuwa ne a yayin da Burundi ke nuna tirjiyar zuwan sojojin a gabanin taron kungiyar da zai gudana a birnin Adis Ababa na kasar Habasha a karshen makon nan.

Muhimman batutuwan da zasu mamaye taron kungiyar kasashen Afrikan 54 dai sun hada da kare yancin jama’a tare da duba irin rikice- rikicen da ke addabar wasu daga cikin kasashen Afrikan.

Taron wanda za a gudanar a ranakun Asabar da Lahadi zai kuma gudanar da wani sabon zaben da zai samar da sabon shugaban kungiyar da zai maye shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe gami da gudanar da tattaunawar da za ta kawo karshen shirin zaman lafiyar Sudan ta Kudu daya ki ci ya ki cinyewa.