Burundi : An kashe ministan muhalli | Labarai | DW | 01.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Burundi : An kashe ministan muhalli

'Yan sanda a Burundi sun bada sanarwa cewar wani mutumin dauke da bindiga ya harbe ministan muhalli da samar da ruwan sha na kasar Emmanuel Niyonkuru har lahira a Bujumbura babban birnin kasar.

'Yan sanda sun ce an kashe ministan dan shekaru 54 a lokacin da ya ke dawo gida a daran jiya, sai dai sun ce sun kame wata mata da ke tare da shi cikin mota a lokacin da harin ya afku. Wannan hari shi ne na farko da aka kai a kan wani ministan a Burundi tun lokacin da kasar ta fada cikin wani hali na rikicin siyasa bayan da shugaba Pierre Nkurunziza ya yi tazarce.