Kungiyoyin kasa da kasa na fuskantar kalubale a Burundi
September 28, 2018Talla
Burundin ta dauki wannan mataki ne har lokacin da dokar da ta kayyade ayyukan kungiyoyin za ta soma aiki. bayan dai wani bincike ne da kwamitin tsaro na kasar ta Burundi ya gudanar kan ayyukan kungiyoyin, ya gano cewa akasarin kungiyoyin ba su bin dokokin kasar ta Burundi kaman yadda babban sakataran gudanarwa na kwamitin tsaron Janar Sisas Ntigurirwa ya sanar yayin wani jawabi da ya yi ta gidan talbijin na kasar ta Burundi, wanda ya ce sake komawar kungiyoyin kan ayyukansu zai ta'allaka ne ga yadda suka aminta da sabuwar dokar. Sai dai tuni wasu jam'an diflomasiyya ke nuna shakkunsu kan lamarin na ganin wannan sabon mataki na da gwamnatin ta Burundi ta dauka ka iya sanya wasu kungiyoyin su rufe ma'aikatunsu a kasar.