Burundi : Al′umma na zaune cikin fargaba | Siyasa | DW | 15.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Burundi : Al'umma na zaune cikin fargaba

Tun bayan yunkurin juyin mulki da bai sami nasara ba, mazauna kasar ta Burundi ke ficewa zuwa makwabtan kasashe irinsu Tanzaniya, domin samun mafaka.

Pierre Nkurunziza, Präsident von Burundi

Shugaba Pierre Nkurunziza

Hayaniyar masu zanga-zanga ake ci gaba da gani kan titunan birnin Bujumbura na kasar ta Burundi, domin cigaba da nuna rashin amincewarsu da wannan yunkuri na shugaba Pierre Nkurinziza da ke neman tazarce a karo na uku, kuma tare da nuna goyon baya ga gamayyar sojojin da suka kuduri wannan aniya ta juyin mulki tun da farko. Hakan na zuwa ne duk kuwa da nutsuwa da ake cewa an fara samu a kasar ba kamar kwanakin da suka gabata ba.

Wani cikin masu wannan zanga-zanga da bai bayyana sunan sa ba na da ra'ayi kamar haka:

“Muna murna da sojojin da sukayi wannan yunkuri, kuma sun sanya mu yin alfahari da kawunan mu".

Wasun kuwa cewa suka yi zasu ci gaba da nuna kin jinin wannan gwamnati ko da kuwa za'a kashesu gaba-daya, abin da suke nema bai wuce zaman lafiya ba dan haka suka dau lokaci suna addu'a.

Ficewar masu fargabar barkewar yaki

Burundische Flüchtlinge in Ruanda

'yan gudun hijira na ficewa daga Burundi

Watakil hakan na da nasaba da tsoron da mutanen garin suka fara ji wanda tun farkon sanar da wannan zance na juyin mulki, dubbunnai daga cikinsu suka fara ficewa daga wannan gari na Bujumbura, amma daga wadanda suka rage, suma a cike zukatansu suke da tsoron abin da kaje ya zo. Kamar yadda Amani Ramadan wani mazaunin birnin Bujumburan ke bayyana wa.

“Abubuwan da kunnuwanmu ke jiye mana kwanaki biyu zuwa uku da suka gabata, shi ne rugugin harbe-harben bindiga da fashewar wasu abubuwa masu karfi, mun kuma ji hayaniyar masu zanga-zanga, babu inda muka iya motsawa sabo da 'yan kwanakin nan anyi rikici sosai, amma dai mun godewa Allah tunda muna raye.

Wasu rahotanni dai sun nuna cewa shi kansa jagoran masu yunkurin wannan juyin mulkin wato Major General Godefroid Niyombare ya shiga hannun dakarun sojin da ke goyon bayan shugaba Nkurunziza. Kafin wannan lokaci dai ya yi wasu kalamai da suka karawa miya gishiri a wannan tashin-tashina:

An yanka ta tashi

Burundi Militärputsch

Sojin da su ka yi ikirarin juyin mulki

“A madadin kwamitin bada kariya na kasa, zamu yi komai a karkashin ikonmu domin mu kare jama'armu, kuma zamu yi aiki da dumbin al'ummar Burundi, wadanda alhakinmu ne mu kare su kamar yadda muka yi a kasashe irin su Somaliya, nanma ya rataya a wuyanmu mu kare ‘yan kasar mu, ‘ya'yan mu da iyayen mu, Na gode muku”.

Sai-dai kuma mai Magana da yawun shugaban kasa Nkurunziza wato Garvais Abayeho, ya gaya wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, "Jagoran masu juyin mulkin Niyombare kama shi aka yi, bawai shi ne ya mika kansa da kansa ba, kuma shi da sauran abokansa cikin wannan aiki da wasunsu suma sun shiga hannu, za su fuskanci hukunci gaban shari'ah dai-dai da abin da suka aikata".

Sauti da bidiyo akan labarin