Burtaniya za ta dakatar da bai wa Israila wasu makamai
September 2, 2024Sanarwar ta biyo bayan nazarin da ma'aikatar harkokin wajen Burtaniya ta yi kan sayar wa Israila makamai da yadda ta ke amfani da su a yakin da ta ke yi da Hamas a zirin Gaza.
Sakataren harkokin wajen Burtaniya David Lammy ya shaida wa majalisar dokoki cewa Burtaniya za ta soke lasisi 30 daga cikin 350 na makaman da za ta sayar wa Israila.
Ya ce dakatarwar na wucin gadi zai kunshi makaman da za a iya yin amfani da su a yakin da ake yi yanzu a Gaza da suka hada da Jiragen yaki da jirage masu saukar ungulu da kuma jirage marasa matuka.
Sai dai kuma haramcin bai hada da sassan jiragen yaki samfurin F-35 ba.
Lammy ya kara jaddada kudirin Burtaniya na goyon bayan Israila ta kare kanta yana mai cewa dakatar da bai wa Israila makaman na wucin gadi ba zai yi wani babban tasiri a kan tsaron Israilar ba.
Gwamnatin Labour ta Burtaniya ta sha kiran tsagaita wuta a yaki tsakanin Israila da Hamas tare da hanzarta kai kayan agaji zuwa Gaza tun bayan da ta hau karagar mulki a ranar 5 ga watan Yuli.