1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burtaniya na fuskantar kalubalen tsaro

Ahmed SalisuNovember 24, 2014

Burtaniya ta ce sha'anin tsaronta na cikin gida na fuskantar babban kalubalen da bai taba cin karo da irinsa ba tun bayan harin nan na 11 ga watan Satumbar 2001 da aka kai Amirka.

https://p.dw.com/p/1DsDw
EU Gipfel 23.10.2014 Cameron
Hoto: Reuters/Francois Lenoir

Sakatariyar harkokin cikin gidan Burtaniyar Theresa May ta ce jami'an tsaron kasar sun tabbatar musu cewar lamuran tsaron kasar na fuskantar wannan kalubale ne daga 'yan ta'adda don haka abu ne da May din ta ce ya kyautu a dauka da muhimmancin gaske.

Ms. May ta ce a saboda haka ne ma London za ta dauki matakai na ganin ta dakile duk wani aiki na ta'addanci kuma ma tuni ta kammala shirye-shirye na mika wani kuduri ga majalisar dokokin kasar wanda ya danganci yaki da ta'addanci.

Kudurin dai inji sakatariyar harkokin cikin gidan ya hada da dabaru na kawar da duk wata barazana da za a iya fuskanta daga 'yan kasar da suka dawo gida daga Siriya da Iraki musamman ma wanda suka tallafawa kungiyar nan ta IS a fafutukarta ta kafa daular Musulunci.