1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso ta shiga makoki bayan harin ta'addaci

Salissou Boukari
August 17, 2017

Harin ta'addancin da wasu da ake zargin mayakan jihadi ne suka kai a birnin Ouagadougou ya hallaka mutane 18 a wani gidan cin abinci na Turkawa da ake kira "Cafe Restaurant Aziz Istanbu".

https://p.dw.com/p/2iPaV
Terroranschlag in Burkina Faso
Hoto: Reuters

Wani batun na daban da ke ci gaba da haifar da muhawara biyo bayan wannan hari na Cafe Restaurant Aziz Istanbul, shi ne na dalilin da ya sanya a ka kai shi, inda yayin da wasu ke cewa harin ta'addanci ne na masu kishin Islama, wasu na dora alhakin hari ga tsohuwar gwamnatin Blaise Compaore.