1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nemi a kamo Blaise Campaore a ko'ina

Yusuf BalaDecember 21, 2015

Shugaba Campaore da juyin juya hali a Burkina Faso ya yi awon gaba da mulkinsa a yanzu sammacin kasa da kasa ya hau kansa.

https://p.dw.com/p/1HRPN
Burkina Faso Ex-Präsident Compaore Archiv 2011
Blaise CompaoreHoto: picture alliance/AP Photo/R. Blackwell

Kasar Burkina Faso ta gabatar da takardar sammaci ta kasa da kasa wacce ke bukatar a kama tubabben shugaban kasar Blaise Compaore, a kamun da ke da alaka da kisan tsohon shugaban kasar Thomas Sankara kamar yadda majiyar shari'a ta fada wa kamfanin dillancin labaran Reuters a ranar Litinin din nan.

Lauya da ke bangaren iyalan tsohon shugaban kasar ta Burkina Faso Thomas Sankara wato Prosper Farama, ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labaran Reuters wannan labari inda ya ce an sanya takardar sammacin ne ta kasa da kasa a kan shugaba Campaore a cewar alkali mai bincike.