Burkina Faso ta fada rikicin siyasa | Labarai | DW | 22.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Burkina Faso ta fada rikicin siyasa

'Yan adawan Burkina Faso sun nuna rashin yarda da gyaran kundin tsarin mulki

Jam'iyyun adawa na kasar Burkina faso sun zargi Blaise Compaore da neman kyara wa kundin tsarin mulki ta hanyar da ta saba doka, domin ya samu damar ci gaba da mulkin kasar da ke yankin yammacin Afirka.

Madugun 'yan adawa Zephirin Diabre ya nemi zanga-zanga ta kasa baki daya, saboda nuna rashin yarda da duk wani yunkurin da kawarda wa'adin da shugaban kasa zai yi kan madafun iko. Compaore ya shafe shekaru 27 yana mulkin kasar kuma yana taka mahimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin, amma yunkurin kiran zaben raba gardama kan kundin tsarin mulki ya raba kan al'ummar kasar.

An fara samun tayar da jijiyar wuya tun lokacin da gwamnatin kasar ta Burkina Faso ta ce za ta mika shirin gyaran fuska wa kundin tsarin mulki domin Shugaba Blaise Compaore ya sake takara a zaben shekara mai zuwa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba