1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon hari a Burkina Faso

Zulaiha Abubakar
January 17, 2020

Sojoji biyar sun mutu sakamakon bi ta kan nakiya da motar da suke ciki ta yi kamar yadda hukumar tsaron kasar ta sanar a wannan Juma'ar.

https://p.dw.com/p/3WNYd
Symbolbilder Niger Armee
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Kasashen  Burkina Faso da Mali da kuma Jamhuriyar Nijar na fuskantar ayyukan ta ta'addanci daga masu tattsauran ra'ayin addini, al'amarin da ya sanya al'ummar kasashen bayyana shakku game da aikin tsaron da sojojin Faransa ke yi a yankin na Sahel. Ya zuwa yanzu dai babu kungiyar da ta sanar da daukar alhakin wannan hari.