Burkina Faso: Hari kan masu mahaka ma′adanai | Labarai | DW | 07.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Burkina Faso: Hari kan masu mahaka ma'adanai

Masu aikin hakar ma'adanai kimanin 37 ne suka halaka a sakamakon wani harin kwanton bauna da mayakan jihadi suka kai kan ayarinsu a wani yanki mai suna Tapoa.

Shugaban kamfanin da mallakin wasu 'yan Kanada ne , ya ce, akwai tagawar jami'an tsaro da ke rakiyar ma'aikatan a yayin harin, sai dai wani jami'in tsaron kasar ta Burkina Fason, ya ce motocin sun taka abubuwan fashewa da mayakan suka riga suka dasa ne a kan hanyar. Gwamnatin kasar mai fama da tashe-tashen hankula daga masu tayar da kayar baya a kasashen yankin Sahel, ta ce harin ya kasance mafi muni da kasar ta fuskanta a cikin shekaru biyar. Semafo mallakin wasu 'yan kanada ne da ke da kamfanonin hakar ma'adanai biyu a cikin kasar. A safiyar jiya Laraba aka kai harin da ya kara tayar da hankula al'umma a yankin.