1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'umma na tserewa daga arewcin Burkina Faso

Zulaiha Abubakar MNA
December 26, 2019

Majalisar Dinkin Duniya tare da shugaban Kristoci mabiya darikar Katolika Fafaroma Francis, sun yi Allah wadai da mummunan harin da 'yan ta'adda suka kai a Burkina Faso a lokacin da ake bukukuwan Kirsimeti.

https://p.dw.com/p/3VL0g
Symbolbild- Nigera - Militärübung
Hoto: picture-alliance/dpa/P. de Poulpiquet

Shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore ya sanar da ranaikun Laraba da wannan Alhamis din a matsayin lokutan alhini a fadin kasar biyo bayan harin ta'addancin da ya yi sanadiyyar rasuwar mutanen da yawansu ya kai 42 wadanda suka hada da sojojin kasar bakwai.

Yankunan da ke kan iyakokin kasar ta Burkina Faso da Mali da kuma Jamhuriyar Nijar na fuskantar hare-hare tun a shekara ta 2015, lokacin da masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama suka billa a yankin na Sahel.

A farkon watan Disamban nan ne shugabannin kasashen kungiyar G5 Sahel suka gudanar da taro a Jamhuriyar Nijar don bukatar karin hadin kai tsakanin kasashen da kuma neman taimakon kasashen ketare a yaki da ayyukan ta'addancin da ke tsananta a yankin.

Wannan mummunan al'amari na ci gaba da haifar da fargaba tsakanin mazauna yankunan duk kuwa da cewar akwai sojojin Faransa akalla dubu hudu da dari biyar jibge a yankin suna aikin tsaro.