1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harbe-harbe a kusa da fadar mulki a Ouagadougu

Binta Aliyu Zurmi
September 30, 2022

Rahotanni daga Burkina Faso na nuni da cewar da sanyin safiyar wannan rana ta Juma'a an ji karar harbe-harbe a kusa da fadar shugaban kasa da kuma wasu yankunan sansanin sojoji.

https://p.dw.com/p/4Hb3L
 Colonel Paul-Henri Damiba
Hoto: Luc Gnago/REUTERS

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito cewar tuni sojoji suka tare wasu manyan hanyoyi da ke isa zuwa fadar gwamnati da ta manyan gine-ginen gwamnati.

Babu tabbacin ko wannan harbe-harben na da alaka da yunkurin juyin mulki, sai dai batun na da rikitarwa da ma rashin sanin tabbas. 

Rahotannin sun tabbatar da cewar illahirin gidajen talabijin da na radiyo basa aiki a yanzu haka.

Al'umma a kasar na cikin halin dar-dar na rashin sanin takamaimai me ke faruwa, sai dai an tabbatar da baza sojoji a lungu da sako musamman a fadar gwamnatin ta Ouagadougu.