Bunkasar fasaha a Afirka | Zamantakewa | DW | 19.02.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Bunkasar fasaha a Afirka

Makarantun a nahiyar Afirka, na kara samun ci-gaba ta fannin fasahar zamani, inda yanzu a kasashe dadama ake bada darasi bisa na'ura mai kwakwalwa

Bayanai dai na nuna cewar ana samun ci gaba mai ma'ana ta fuskar sadarwa a nahiyar Afirka, musamman saboda karuwar masu amfani da wayar tafi da gidanka ko Salula. Sai dai kuma abin da wasu ke tambaya shi ne wane tasiri ne hakan ke da shi ga bangarorin rayuwar jama'a, kamar fannin ilimi.

Misali a Namibiya

Ana ta jita-jita akan karatun zamani a nahiyar Afrika, musamman yanzu da farashin katin waya ke kara hawa. Kapenda wani mai gabatar da kansa a bidiyo ta Youtube, dan shekaru 19 ya kammala karutunsa a makarantar gwamnati da Windhuk babban birnin kasar Namibiya, kuma ya kasance kyakyawan misali kan yadda Nahiyar Afrika ke sauyawa, kafafen yada labarai na mai da hankali kan matasa.

Afrika na fuskantar kalubale ta bangaren rashin wadatacen wutan lantarki, yayin da tsofaffin malaman makaranta, suke amfani da kayan koyarwan gargajiya, wajen koyarwa dalibai wadda yake janyo koma baya wa dalibai a yankin. Inda Kapenda yace.

"A makarantar mu dai muna da sabbin na'urorin koyon darasi da sauransu, a da dalibai masu karantar na'ura mai kwakwalwa ne kawai suke amfani da inji mai kwakwalwar. Amma yanzu an samu ci gaba inda kowa a makarantar yake amfani da na'ura mai kwakwalwa, wajen aiki ko neman karin bayani akan wani al-amari,. Wasu daga cikin malaman kan yi amfani da bidiyo wajen koyarwan wasu darusan".

Mafi akasarin malaman makarantu a birnin Windhuk, suna amfani da na'ura mai kwakwalwa wajen koyarwa, wadda ba abun mamaki bane a kasar ta Namibia.

Misali a Najeriya

Iyke Chukwu ma'aikaci ne a hukumr makarantun sakandare a Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya, yana daya daga cikin masu koyar wa malamai tsarin koyarwa na zamani wato "Hukumare Digital".

"Shekaru biyu da suka wuce babban birnin Tarayyar Najeriya wato Abuja, ta kokarta wajen aiwatar da karatun kimiyya a manyan makarantun sakandare, ta hanyar sanya na'ura mai kwakwalwa a makarantu. Amma matakin farko da suka dauka shi ne koyawa malaman makarantun karatun kimiya, domin ya kamata su kasance suna da basira sosai akan kimiya, don su koyarwa daliban da ke makarantu".

Ya kamata ace malaman makarantu sun samu ilimin kimiya, kana su kasance sun iya amfani da na'ura mai kwakwalwa, domin za ta taimaka musu wajen karin bayani akan ayukansu, kuma domin su koyar da dalibansu aiki da ita.

Mawallafa: Chiponda Chimbelu da Zainab Babbaji Katagum

Edita: Usman Shehu Usman