1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron tattalin arzikin Chaina da Afirka

Ramatu Garba Baba LMJ
September 3, 2018

An bude taron koli tsakanin Chaina da kasashen Afirka da ya hada kan shugabanin kasashen na Afrika a birnin Beijin na Chaina, da nufin inganta sha'anin tattalin arzikin nahiyar Afrika.

https://p.dw.com/p/34EFt
China-Afrika-Gipfel in Peking
Hoto: DW/S. Mwanamilongo

Chaina dai ta kasance kasar da ta sha gaban sauran kasashen duniya ta fuskar zuba jari mai yawan gaske da ke kuma bunkasa tattalin arzikin kasashen nahiyar ta Afrika. Shugaban kasar Chaina Xi Jinping dai a wannan Litinin, ya bude taron ne da yi wa Afrika albishir na bayar da tallafin kudi na dala biliyan sittin a kokarin son bunkasa tattalin arzikinsu. Shugaban bai yi wata-wata wajen karyata jita-jita na yunkurin kasarsa a son yin katsalandan cikin sha'anin mulkin kasashen na Afrika ba. Xi ya ce kudin Chaina ba ya dauke da tukwici na son zuciya. A yayin da manazarta ke nuna fargaba kan yawan dogaro da karbar bashi daga Chaina duk da cewa bashin da Chainan ke bayarwa babu ruwa cikinsa, shugabannin Afirka sun yi watsi da ikirarin, maimakon hakan sun karkata hankulansu kan alfanun da ke tattare da wannan dangantaka da Chaina.

Äthiopien Industriepark Hawassa
Babbar masana'anta da Chaina ta gina a HabashaHoto: Imago/Xinhua/M. Tewelde

A jawabinsa ma dai, shugaban kasar Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya soma ne da jan hankula tare da musanta rade-radi kan mamayar ayyukan kasar Chaina a nahiyar Afirka, abin da wasu ke kallo da wata sabuwar dabara ce mai kama da son yin mulkin mallaka. Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da samun takun saka a tsakanin Amirka da Chainan, inda kasashen biyu suka dauki matakan karawa kayayyakin da ke shiga kasashen juna kudadden haraji. A nasa bangaren Shugaba Paul Kagame na Ruwanda kuma shugaban kungiyar Tarrayar Afrika, ya yi jinjina ga Chaina kan tsarin nan na inganta abubuwan more rayuwa da ta kirkiro da aka yi wa lakabi da "Belt and Road Initiative." Kagame ya jaddada alfanun tsarin ta fuskar bunkasar tattalin arziki dama ci-gaba ga nahiyar ta Afrika.

Ruanda Besuch Präsident Xi Jinping China
Shugaban Ruwanda kana shugaban kungiyar Tarayyar Afirka Paul Kagame da shugaban kasar Chaina Xi JinpingHoto: Getty Images/AFP/S. Maina

Tsarin na  dai na "Belt and Road Initiative," zai samar da hanyar bunkasa sha'anin kasuwanci a tsakanin kasashen walau ta hanyar sufuri ta sama ko ta ruwa, wanda a dalilin hakan ne Chaina ta yi wa kasashen na Afrika tayin ba su basussuka na makudan kudi, musamman ga kasashen da ke fuskantar karancin kudi. A na shi bangaren kuwa sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres da ya halarci taron ya jaddada goyon bayan majalisar wajen ganin kasashen Afrika sun cimma burinsu ta hanyar amfani da wannan dama da suka samu daga kasar Chaina. A baya dai Chaina ta soke basussukan da take bin kasashen Afrika da ke fama da talauci. Baya ga haka ma dai gwamnatin Beijing na kara duba bangaren tsaro, inda a shekarara da ta gabata ta soma bude sansanin sojojin ruwa a kasar Djibouti tare kuma da tallafawa sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da aikin tsaro, baya ga shirin bunkasa cinikayyar makamai da ta soma tun daga shekarar 2008.