Bunkasa al′ada a Guinea | Himma dai Matasa | DW | 05.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Bunkasa al'ada a Guinea

A kasar Guinea da ke yammacin Afirka, an sami wata Zeinab Koumanthio Diallo da ke harkar rubuce-rubuce wadda kuma har ila yau ke shugabantar wata cibiyar adana al’adu na al’umar Fulani.


kasar ta Gini, inda take kokarin adana tare da bayyana al’adun al’umar da aka fi saninsu da riko ga harkar kiwo kuma shekaru 10 da suka gabata bayan aiki a kungiyoyin kasashen duniya ta koma gida. Ita dai Zeinab Kumantiyo Djallo, ta gina wani gidan adana tare da taskance al’adun al’umar Fulani ne a wani wajen da ake kira Labé, wajen da ake iya zuwa don kallon kayan asali na fulanin. A halin yanzu ma wajen ya bunkasa day a zama babbar cibiya ta al’adu.

Zeinab Koumanthio Diallo na gamuwa da mutane da yawa, a ziyarar da take kai wa wurare daban daban na neman kayayyakin Fulani da za ta yi ajiyarsu a cibiyar da ta kafa.

Tana fatar matan da take ganuwa da su su rika bata kayayyakin domin adanawa. Babban sha’awar abubuwan da ake yin a hannu da kuma wadanda ake amfani da su yau da kullum.

 

Zainab musamman tana karfafa ‘yan mata wajen fahimta tare da fassara rubutattun tarihin al’adunsu don dorewar aniyar. Ta hakan ne take basu kwarin guiwa a al’umar da akasari maza ne ke a sahun gaba. Wannan yarinyar mai shekaru 17
Dalanda Dieng bat a shakkar al’adunsu na bukatar taskancewa.

Al’adar al’umar Fulani dai, al’ada ce da ke kunshe da tsarin addinin Islama. Bayan zuwa hajji a 2011, Zeinab Djallo ta kuma bude makarantar muhammadiyya a garin Labe, inda ake koyar da ‘yan mata ilimi. Suna kuma fahimtar ‘yancinsu dama fahimtar duniya baya ga ilimin addini.

Yanzu dai galibin ‘yan matan da suke karatu a wannan cibiyar, suna da fahimtar irin rayuwar da suke muradi, saboda al’adu ba su taka masu birki, musamman wajen koyoyn sana’a. Wasu daga ciki sun yanke shawarar koyon aikin kafinta.