1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Tana kasa tana dabo a gasar Bundesliga ta Jamus

Mouhamadou Awal Balarabe MNA
April 12, 2021

Kolon ta kori kocinta bayan da ta sami kanta a matsayin kusa da na karshe na Bundesliga, yayin da RB Leipzig ta rage ratar da ke tsakaninta da Bayern Munich a saman teburi.

https://p.dw.com/p/3rsIp
Deutschland Bundesliga - 1. FC Köln v 1. FSV Mainz 05 | Markus Gisdol
Hoto: Thilo Schmuelgen/dpa/picture alliance

Za mu fara da Afirka, inda aka gudanar da zagaye na biyu na wasan neman hayewa matakin kwata-fainal na gasar zakarun kwallon kafa na wannan nahiya. A wasannin na karshen mako, kungiyar Belouizdad ta Aljeriya ta bai wa marada kunya, inda ba za to ba tsammani ta doke Mamelodi Sundows ta Afrika ta Kudu da ci 2-0, lamarin da ya sa ta samun jimillar maki tara a rukuninta na biyu. Wannan yana nufin cewa Belouizdad ta bi sahun Mamelodi mai maki 13 wajen kai wa matakin kwata fainal. Yayin da TP Mazembe ta kwango ta gaza kaiwa gaci duk da ta samu nasara a kan Al-Hilal ta Sudan ci 2-1, saboda maki biyar kacal da take da shi.

A rukuni na hudu ma, wata kungiyar ta Aljeriya wato MC Alger ta kai labari bayan da ta tashi kunnen doki 1-1 a ranar Asabar a Tunis a karawa da Esperance, saboda wannan nasara ta bai wa MCA damar samun maki tara, tare da kasancewa a bayan Esperance ta Tunisiya wacce dama take da tikitin hayewa mataki na gaba na gasar zakarun kwallon kafar Afirka. A wannan rukuni dai Zamalek ta Masar ta lallasa Teungueth ta Senegal da ci 4-1, amma bai wadatar wajen samun biyan bukata ba.

'Yan wasan Zamalek a karawarsu da kungiyar al-Ahly, ta cin kofin zakarun Afirka a watan Nuwambn 2020 a birnin Alkahira.
'Yan wasan Zamalek a karawarsu da kungiyar al-Ahly, ta cin kofin zakarun Afirka a watan Nuwambn 2020 a birnin Alkahira.Hoto: Sameh Abo Hassan/dpa/picture alliance

A rukunin na uku kuwa, Al-Ahly da ke zama giwar kwallon kafar Afirka ta doke Simba ta Tanzaniya da daya mai ban haushi, yayin da AS Vita Club ta DR Kwango ta yi wa Al-Merreikh ta Sudan cin kaca 3-1.

A Takaice dai kungiyoyi uku ne suka samu tikitin zuwa matakin kwata fainal na gasar zakarun Afirka ciki har da Belouizdad da MC Alger da kaizer Chief, baya ga biyar da aka riga a samu tun da farko.

A gasar neman cin kofin Hukumar Kwallon kafa ta kasashen Afirka da aka fi sani da Confederation Cup, kungiyar Coton Sport ta Garouan Kamaru na ci gaba da jan zaranta ba tare da ya tsinke mata ba, inda bayan wasanni hudu da aka buga a matakin rukuni, ta lallasa Napsa Stars ta Zambiya da 5-1. Su kuwa Js Kabylie ta Aljeriya da RS Berkane ta Moroko suka tashi ba wanda ya ci wani.

Yayin da Enyimba ta Najeriya ta yi abin fallasa inda ES Steif ta Aljeriya ta gasa mata aya a hannu da 3-0. Ita ma Orlando Pirates ta Afirka ta Kudu ta yi wa Alhi Benghazi ta Libiya kaca-kaca 3-0. A rukuni na uku kuwa, Ndola Nkana ta Zambiya ta sami nasara a kan Namungo ta Tanziya da ci daya mai ban hashi, Pyramids ta Masar kuwa ta baras da wasan ci 0-3 a gaban Raja Casablanca. Wannan ne ya sa Raja Casablanca samun damar hayewa zuwa zagaye na gaba.

'Yan mata da ke buga wa babbar kungiyar kwallon kafar Kamaru sun sha kashi ci 2-1 a hannun 'yan matan Chile a zagayen farko na wasannin neman cancantar shigar gasar Olympik da za ta gudana a birnin Tokyo na kasar Japan. A halin yanzu dai 'yan mata Zambiya ne kawai za su wakilci nahiyar Afirka a rukunin mata a wasannin na Olympik. Sai dai an shirya wasannin cike gurbi tsakanin kasashen da suka fi nuna kwazo a wasannin share fage a birnin Antalya na Turkiyya don samar da kasa ta karshe. Amma wannan rashin nasarar ya dagula wa Lionesses na Kamaru lissafi, saboda tana bukatar yin ruwan kwallaye kafin hakarta ta cimma ruwa.

Kungiyar Bayern München na ci gaba da jan zarenta a gasar Bundesliga ta Jamus
Kungiyar Bayern München na ci gaba da jan zarenta a gasar Bundesliga ta JamusHoto: Andreas Gebert/AFP

A nan Jamus, 'yan kwanaki bayan shan kaye a hannun Paris Saint-Germain a gasar cin kofin zakarun Turai, Bayern Munich ta yi tuntube a karawar da ta yi da Union Berlin a filin wasa na Allianz Arena, inda aka tashi ci daya ko ta'ina a wasan mako na 28. Duk da cewa tana ci gaba da kasancewa a saman teburi da maki 65, amma kuma biyu daga cikin 'yan wasanta Kingsley Coman da Jérôme Boateng sun samu rauni a wasan na ranar Asabar, lamarin da ya sa aka fitar da su. Wannan halin na rashin lafiyar 'yan wasa na matukar damun kocin Bayern, Hansi Flick, saboda 'yan wasa da yawa da suka hada da Robert Lewandowski da Leon Goretzka ba sa wasa saboda suna jinya. Sai dai kuma a daya hannun ya ba da dama ga matasan 'yan wasa kamar Jamal Musiala, wanda ya zira kwallon damar haskawa. Ko da Thomas Müller sai da ya yaba rawar da matasan 'yan wasan bayern suka taka.

Ala kulli halin dai, wannan kunnen doki da Bayern Munich ta yi ya sake dagula lamura a Bundesliga, saboda RB Leipzig da ke a matsayi na biyu bayan nasara da ta samu a kan Werder Bremen da 4-1 tana da ratar maki biyar ne kacal da yaya babba, saboda haka har yanzu ba a san maci tuwo ba, a daidai lokacin da ya rage wasanni takwas a kammala kaka.

Bayan Bayern Munich da RB Leipzig, Wolfsburg ta ci gaba da rike matsayinta na uku da maki 54 duk da doketa da Eintracht Frankfurt ta yi da ci 4-3 . Wannan nasarar ta tabbatar da kyakkyawar rawa da Frankfurt ke takawa tun bayan dawowa hutun lokacin sanyi, lamarin da ke dada buda mata hanyar cancantar zuwa Gasar Zakarun Turai. A halin yazu ma dai 'yan wasan Frankfurt na da ratar maki bakwai a gaban Borussia Dortmund wacce da gumun goshi ta doke VfB Stuttgart 3-2.

Dan wasan tennis Hideki Matsuyama ya zama dan kasar Japan na farko da ya ci kofin Augusta Masters na 85 da ya kammala a ranar Lahadi a Georgia na kasar Amirka. Shi dai dan wasan mai shekaru 29 ya doke Ba'amirke Will Zalatoris, lamarin da ya ba shi damar maye gurbin dan Amirka Dustin Johnson da ke da matsayina 25 a duniya. Amma wannan nasarar ita ce mafi daraja ga dan wasan tennis da ya fito daga Japan.