1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bundesliga: Lewandowski ya ci kwallaye 300

Abdul-raheem Hassan
January 16, 2022

Dan wasan gaba na kungiyar Bayern Munich Robert Lewandowski, ya zama dan wasa na biyu da ya zura kwallaye 300 a gasar Bundesliga cikin wasanni 333.

https://p.dw.com/p/45bOt
München | Bundesliga | Robert Lewandowski
Dan wasan Bayern Munich, Robert LewandowskiHoto: Sebastian Widmann/Getty Images

Robert Lewandowski ya taka rawar gani a wasan da Bayern Munich ta doke Hertha Berlin da ci 5-0, bayan mintuna 30 da kwallon farko da Thomas Müller ya farke wa Bayern, Lewandowski ya kara ta biyu da bugun kai (heading).

A hutun rabin lokaci, Moller da Leroy Sané suka sake garawa Lewandowski kyaftin din Poland ya zura kwallo ta biyu a wasan, wanda ya bashi damar samun kwallaye 300 gaba daya a kungiyar FC Bayern.

Ta haka ne Lewandowski ya kai wannan matsayi a wasanni 333 kacal, inda ya ke shan kwallo akalla daya a kusan kowane wasa. Dan wasan ya kuma taimaka an sha kwallaye 65.

Duk da cewa an dade ana irga kuri'a amma nasarar Robert Lewandowski na cika kwallaye 300, wata nasara ce ta cancantar cin kyautar gwarzon dan wasan duniya.