Bunƙasa samar da nonon dabbobi a Nijar | Noma da Kiwo a Afirka | DW | 23.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Noma da Kiwo

Bunƙasa samar da nonon dabbobi a Nijar

Makiyaya da hukumomi a garin Kollomma dake kusa da birnin Tahoua sun duƙufa wajen gano hanyar bunkasawa da darajanta aikin samar da nono daga bisashe.

A Jamahuriyar Nijar, a garin Kollomma dake da nisan kilomita goma da birnin Tahoua, aka gudanar da shagulgullan ranar makyaya na gundumar Tahoua wanda shine karo na farko wanda aka ba shi taken darajanta Nono da ake samu daga bisashe.

Aƙalla dai kungiyoyin makiyaya guda ashirin ne suka hade suka zama tsintsiya maɗarminki ɗaya domin duba ƙibla guda da zimmar neman bakin zaren matsalolin samar da isasshen nono daga bisashe da ake fuskanta cikin wannan ƙasa ta Nijar, ganin yadda a kullu yaumin ake waƙar cewa Nijar ƙasa ce ta Noma da Kiwo kuma a fannin kiwo sanin kowa ne Nijar ta yi fice wajan yawan dabbobi, sai dai a kullu yaumin ana odar nono daga kasashen waje. Boubakar Moussa memba ne a hadaɗɗiyar ƙungiyar makiyayan gundumar Tahoua.

Fatan kawo karshen odar nono daga waje

Ya ce: "Gamu da shanu da yawa, gamu da rakumma da yawa, awaki, tumaki da yawa amma nono sai dai mu yo odar shi daga wani wurin da bamu ma san ina ne ba, dan haka muna ganin cewa wannan wata dama ce ta janyo hankalin ƙungiyoyi masu hannu da shuni ta yadda za su kama musu dan su rinka samun nono sosai dan su ci da kansu."

Hukumomi dai a jamhuriyar Nijar ta hanyar ma'aikatar kula da arzikin dabbobi na iyakar ƙoƙari na ganin cewa an samu ci gaban kiwo ta hanyar wayar da kan makiyaya da dai sauransu, kuma da yake har yanzu da sauran rina cikin kaba amma a cewa Dr. Issiyaku Salifou daraktan ma'aikatar kula da arzikin dabbobi ta gundumar Tahoua, cewa yayi shi dai batun inganta nono batu ne na gari domin idan ya bunƙasa, to zai sanya makiyaya su yaƙi talauci tare da rage sayar da dabbobin su.

Ya ce: "A cikin tafiyar tsarin rayuwar yanzu da take taɓarɓarewa talauci yayi yawa, idan aka biyo ta wannan hanya za ka ga nono zai yi daraja mai yawa, idan aka bi hanyoyin sarrafa shi ana yin kamar su cukku, ko yogot da dai sauran su ka gani zai kare wasu kananan saye da sayarwa na cikin gida, idan musali mace na sai da nono sai shi kuma miji ya sayar da cuku a bakin shagon sa."

Sai dai daga na su ɓangare makiyayan duk dai da cewa sun ba da goyon bayansu tare da haɗa kansu dan cimma gurin da suka sa ma gaba amma suna ganin cewa babbar matsalar su ita ce ta rishin abincin dabobi.

Ra'ayoyin makiyaya a Tahoua

"Sunana Dari Amadu Rugga daga Dakashe, yanzu matsalolin da muke gani, rani yayi yawa, domin daji share shi mutane ke yi amma idan ana barin ciyawa cikin daji to dole dabbobi su samu abinci."

"Sunana Abdullahi komai an kwashe ciyawa an share daga daji an kaita cikin gari, icce an kai gari, ciyawa an kai gari amma sai a ce shekaru sun sake alhali mutane ne suka sake."

"Sunana Alhaji Maude Magaji shugaban makiyayan Tahoua mu abun da muke so a san aikin da muke tun muna cikin wahala a san wadda muke ciki, shi ne muka ƙirƙiro wannan batu na darajanta nono to a kama mana dan a samu ci gaba tun da dai muma 'yan Nijar ne a yi mana yadda ake wa kowa."

Fasahar darajanta nonon dabbobi fusa'ace da ta dade a bisa takardu inda hukumomi ke ganin cewa idan dabbobi na bayar da isasshen nono to wata hanya ce mai ƙarfi ta yaƙi da talauci a wannan ƙasa da a kullu yaumin ake kira ta Noma da Kiwo. Yanzu dai ana iya cewa waɗannan makiyaya sun buɗa wata ƙofa da idan aka bita a tsanake to za ta haifar da walwala a fuskokin makiyaya na birni da na ƙauye.

Mawallafi: Salisou Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin